Gambari Zai Maye Gurbin Muƙamin Abba Kyari

17

A gobe Laraba ne za a sanar da Ibrahim Gambari, Farfesan Kimiyyar Siyasa kuma tsohon babban Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, CoS, jaridar Intanet ta TheCable ta fahimci haka.

Za a gabatar da shi ne a yayin taron tattaunawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, FEC wanda za a yi ta hanyar amfani da fasahar Intanet.

Kodayake dai ba a sanar da muƙamin nasa ba a gwamnatance, TheCable ta tabbatar daga majiyoyin dake Fadar Shugaban Ƙasa cewa zai maye gurbin Abba Kyari, wanda ya rasu sakamakon cutar COVID-19 a watan da ya gabata.

Mista Gambari, haifaffen Ilori dake jihar Kwara, ya riƙe muƙamin Ministan Harkokin Waje a lokacin da Shugaba Buhari yake Shugaban Mulkin Soja tsakanin 1983 zuwa 1985.

A halin yanzu, shi ne wanda ya kafa kuma Shugaban Savannah Center External Link da yake Abuja, wani kamfanin bincike, bada horo da shirya muhawara kan manufofin gwamnati a kan dangantakar diflomasiyya (warware rikici) dimokuraɗiyya da ci gaba a Afrika.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan