Arana Mai Kama Ta Yau 29 Ga Watan Yuni

164

Arana mai kama ta yau a shekarar data gabata ta 2019 ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta sayi Aaron Van-Bissaka daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Crystal Palace wadda take daga ƙasar Ingila.

Manchester United ta sayi ɗanwasanne akan kuɗi £50m domin dawowarsa ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Manchester United dake jahar ta Manchester a ƙasar Ingila, inda yake bugamusu wasa daga baya a ɓangaren hagu.

Ayanzu dai daga shekarar 2019 Van-Bissaka ya bugawa Manchester United wasanni 28 amma baijefa ƙwallo ko guda ba, saidai tun daga lokacin Aaron Wan-Bissaka yafi ‘yan wasan Manchester United da dama ƙoƙari musamman wajen taimakawa a zura ƙwallaye.

Manchester United dai na shirin wakilatar ƙasar Ingila agasar zakarun nahiyar turai akakar wasa maizuwa ta 2020 zuwa 2021 inda take kokawar kasancewa a ‘yan hudun farko.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan