WAEC Za Ta Sa Sabuwar Ranar Fara WASSCE Ta 2020- Gwamnatin Tarayya

186

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce akwai yiwuwar Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Afirka ta Yamma, WAEC ta sauya lokacin gudanar da Jarrabawar Kammala Sakandire ta Afirka ta Yamma, WASSCE, ta 2020.

Ben Goong, Darakatan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya ya bayyana a cikin wata sanarwa ranar Juma’a.

A baya, WAEC ta shirya fara WASSCE ranar 4 ga Agusta, amma Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da cewa ɗalibanta na Makarantun Haɗaka ba za su yi jarrabawar ba saboda COVID-19.

Sanarwar ta ce za a ci gaba da tattaunawa da sauran ƙasashe huɗu da suke rubuta WASSCE, don fitar da sabuwar ranar da za a fara jarrabawar.

Mista Goong ya ce an ba makarantu zuwa 29 ga Yuli, 2020 su tabbatar sun tanadi kayayyakin dawowa makaranta, kamar yadda ƙa’idojin Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa suka shimfida don sake buɗe makarantu cikin aminci.

Ma’aikatar Ilimin ta ce za a ɗauki mataki bayan wa’adin 29 ga Yuli game da dawowar dukkan ɗalibai.

“Mun tuntuɓi masu ruwa da tsaki sosai a ɓangaren ilimi da suka haɗa da Kwamishinonin Ilimi a dukkan jihohin Najeriya, Ƙungiyar Masu Makarantu Masu Zaman Kansu, APSON, Shugabannin Kwalejojin Ilimi, Shugabannin Makarantun Kimiyya da Fasaha, Shugabannin Jami’o’i, wasu gwamnonin jihohi da abokan ci gaba”, in ji sanarwar.

Mista Nwajiuba ya ce sun gana da WAEC ranar Litinin, sun kuma amince su ƙara tuntuɓar sauran ƙasashe huɗu don sa sabuwar ranar jarrabawa.

“Mun ji daɗin damuwar da dukkan masu ruwa da tsaki suka nuna, kuma mun lura da mabambantan ra’ayoyi da aka bayyana game da jarrabawar.

“Muna tabbatar wa iyaye cewa lafiyar ɗalibanmu da ta malamai tana da muhimmanci a gare mu yayinda muke aiki tuƙuru wajen ganin an sake buɗe makarantunmu don ‘yan shekarar ƙarshe su yi jarrabawa”, sanarwar ta ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan