Labaran da jaridar Press Trust of India ta fitar sun rawaito Firaministan jihar Amarinder Singh na cewar, a kwanaki 4 da suka gabata akalla mutane 86 ne suka mutu sakamakon shan giya mara inganci a yankunan Amritsar, Gurdaspur da Tarn Taran.
Singh ya ce a karkashin binciken da aka fara an dakatar da ma’aikatan gwamnati 7 da suka hada da ‘yan sanda.
Firaminista Singh ya bayyana lamarin a matsayin abun kunya, kuma za su saka takunkumai masu tsauri ga wadanda ke jefa rayuwar jama’a cikin hatsari.
A karkashin wasu farmakai da aka fara kai wa an kama mutane sama da 25 tare da rufe wuraren samar da giya mara inganci da dama da ke jihar.

Turawa Abokai