A yau litinin aka bude makarantun sakandare a jihar Kano domin daliban da ke ajin karshe, domin shirye-shiryen tunkarar rubuta jarabawar karshe da za’a fara kasa da makwanni biyu masu zuwa, wadda hukumar shirya jarabawa ta Afrika ta yamma wato WAEC da takwararta ta NECO ke shiryawa a kowacce shekara.
Tun a makon jiya ne wasu daga cikin jihohin ƙasar nan kamar jihohin Jigawa da Lagos suka bude nasu makarantun, bayan cimma yarjejeniya akan haka tsakanin hukumomin ilimi da babban kwamitin yaki da cutar Coronavirus na kasar nan.

A jihar Kano dai jumlar dalibai 27,464 ne daga makarantun gwamnati da na masu zaman kansu za su rubuta jarabawar kammala karatun sakandaren, sai dai gwamnati ta hade cibiyoyin rubuta jarabawar mallakar ta zuwa 33 maimakon 199.
- Yadda Obasanjo Ya Yi Aikin A Daidaita Sahu A Abekuta
- Ina fatan Fim ɗin Lulu da Andalu ya kere sa’a a wannan shekara ta 2022-Jarumi TY Shaban
- Sojan Gona: Kotu a Ilorin ta tura sojan ƙasar Amurka gidan yari
- Yaƙin Rasha Da Ukraine Zai Ci Gaba Da Haifar Da Tsadar Abinci A Afirka
- Hanyoyin da zaku bi domin sabunta katin zabenku
Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano m ta kaddamar da aikin feshin kashe cuttuka da kwari a ajujuwa da harabar makarantun domin tarbar daliban.
Baya ga feshi a makarantun, hukumomin jihar Kano sun ce za su raba takunkumin rufe baki da hanci ga daliban, tare kuma da samar da sinadarin wanke hannu da kuma na’urar auna zafin jikin bil’adama a dukkanin makarantun.