Al’ummar Ƙaraye a jihar Kano su na cikin wahalar rayuwa – Masarautar Ƙaraye

196

Magajin Garin Ƙaraye Injiniya Shehu Ahmad ya bayyana rabon kayan tallafi ga mabukata a cikin al’umma a matsayin wata babbar hanyar yaki da annobar cutar korona.
Injiniya Shehu Ahmad ya bayyana hakan a wajen bikin rabon kayan tallafi kashi na uku wanda ya gudana karamar hukumar Karaye da ke jihar Kano.

Cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na masarauta Karaye, Malam Haruna Gunduwawa ya rabawa manema labarai a masarautar ta Karaye.

Tun da farko Magajin Garin Ƙaraye kuma wanda kuma shi ne hakimin cikin garin Karaye, ya wakilci Sarkin Karaye Alhaji Dakta Ibrahim Abubakar II a wajen taron, ya kuma yi nuni da cewa mutanen da suke karbar tallafin suna cikin farin ciki duba da yadda suke shan wahala wajen samun abincin da za su ci na yau da kullum.

Sannan ya godewa yan kasuwa da kungiyoyin wayar da kan al’umma da dukkan wadanda suka taimaka wajen rage radadin da mutane suke fuskanta sakamakon annobar cutar korona.

Haka kuma Magajin Garin Ƙaraye ya yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su ci gaba da rike wannan tsarin har bayan cutar Corona.

Yayin da take jawabi a wajen taron wanda aka gudanar ana tsaka da ruwan sama, Hajiya Aisha Ja’afar ta ce gwamnatin jijar Kano na shirin bayar da irin wannan tallafi ga magidanta dubu dari uku a fadin jihar Kano.

Shi ma a nasa jawabin shugaban karamar hukumar Karaye Alhaji Abdulhamid Garba Karaye ya bukaci wadanda suka amfana da tallfin da suyi amfani da shi yadda ya kamata kar su siyar da shi.

An raba buhun masara mai girman Kilogram 25 da gero, taliya da man girki ga magidanta 670 a yankin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan