Neymar Yakafa Tarihi Awasan Gasar Zakarun Nahiyar Turai

106

Awasan da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint Germain ta fafata da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Atalanta dake ƙasar Italiya wato wasan kusa dana kusa dana ƙarshe na gasar zakarun nahiyar turai Neymar ya kafa tarihi.

Awasan da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Paris Saint Germain tasha dakyar ahannun Atalanta daci 2 da 1 bayan da Atalanta ta fara jefa ƙwallo kafin atafi hutun rabin lokaci kana daga bisani Paris Saint Germain ta warware ƙwallonta tasake jefa wata acikin mintina uku.

Tarihin da Neymar ya kafa shine yayi cikakken yanka sau 16 atarhin gasar awasa guda 1 kacal adaren jiya inda babu wani ɗanwasa dayayi irin wannan abin atarhihi.

Neymar dai tauraruwarsa ta haska awasan ta yadda ya zamo ta inda yake shiga batanan yake fitaba kuma da taimakonsa PSG takai matakin wasan kusa dana ƙarshe.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan