Ku kiyayi buɗe makarantun Islamiyyu ko kuma ku fuskanci hukunci – Ganduje

139

Hukumar kula da Makarantun Islamiyya da Tsangayu ta Jihar Kano, ta bukaci Makarantun Islamiyya da su guji bude Makarantu domin kaucewa fadawa fushin hukumar.

Shugaban Hukumar Sheikh Gwani Yahuza Gwani Dan Zarga ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da manema da gidan rediyon Freedom da ke Kano.

Gwani Yahuza Gwani Dan Zarga, ya kuma ce rufe Makarantun da budewa yana hannun gwamnatin Jihar Kano, ba wai wasu mutane ba.

Ya kuma ce Malaman Islamiyya masu koyar da tarbiyya, aikin su shi ne umarni da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummunan aiki, ba karya dokar gwamnati ba.

Haka kuma hukumar ta umarci wani shugaban Makarantar Salman Bin Faris dake Unguwar Rijiyar Zaki wanda daya ne daga cikin Malaman da suka bude Makarantar da ya bayyana gaban hukumar domin amsa tambayoyi.

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Yunin da ya gabata ne gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin buɗe wuraren kallon ƙwallo da fina-finai a jihar duk da fargabar yaɗuwar cutar korona.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan