Turkiyya Ta Sake Mayar Da Wata Coci Mai Shekara 600 Masallaci

14

A ranar Juma’a ne Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya fitar da wata doka wadda ta mayar da wata coci mai shekara 600 masallaci wadda take a Santambul, cocin da kuma ta taɓa zama gidan tarihi a 1945,
Wannan coci ba ta da nisa da Hagia Sophia, wata tsohuwar coci da ita ma da aka mayar masallaci a Yuli.

Wata dokar Shugaban Ƙasa da aka wallafa a jaridar gwamnati ta bada umarnin a buɗe Gidan Tarihi na Chora don Musulmi su riƙa salla a ciki.

A cewar dokar, kamar Hagia Sophia, shi ma wannan masallaci za a miƙa shi ga Ma’aikatar Harkokin Addini ta Turkiyya, Diyanet.

Wannan gini mai tarihi wanda aka fi sani da “Church of the Holy Saviour”, mai zane-zane da fenti kala-kala, ya zama Masallacin Ottoman a ƙarni na 16. Gwamnatin Turkiyya kuma ta bayyana shi a matsayin gidan tarihi a 1945.

A Nuwamba, 2019, Kotun Ƙoli ta Turkiyya ta soke wannan hukunci na 1945, abinda ya share hanyar mayar da shi masallaci.

Hagia Sophia, wanda tun farko aka gina shi a matsayin coci a ƙarni na 6, wanda ya zama masallaci, ya zama gidan tarihi, sannan ya ƙera zama masallaci a Yuli da Chora duk Wuraren Tarihi ne da UNESCO ta keɓe.

A watan Yuli, Amurka, Rasha, UNESCO da shugabannin coci-coci daban-daban sun nuna damuwa tare da suka bisa canjin da aka samu a Hagia Sophia, wani babban waje na al’ada ga Kiristoci da Musulmi.

Sai dai Shugaba Erdogan ya yi watsi da wannan suka , inda ya ce hakan katsalandan ne a al’amuran da Turkiyya ke da iko a kai.

Sai dai ba a san yaushe za a buɗe Chora don fara salla ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan