Jonathan Ya Yi Ayyukan Da Suka Ciyar Da Najeriya Gaba— Buhari

106

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi wa tsohon Shugaban Ƙasar, Goodluck Jonathan addu’ar Allah ya ƙara masa tsawon rai da lafiya, a cewar rahoton BBC Hausa.

A wata sanarwa da Sakataren Watsa Labarai na Shugaban, Femi Adesina ya fitar, Shugaban ya yi wannan addu’ar ne yayin da Mista Jonathan zai cika shekara 63 da haihuwa a gobe Juma’a, in ji BBC Hausa.

A cewar BBC Hausa, Shugaba Buhari ya ce ayyukan da tsohon Shugaba Jonathan ya yi sun kawo ci gaba da kuma ɗaga martabar Najeriya.

Shugaba Buhari ya sake jinjina wa Mista Jonathan kan jajircewar da ya yi a matsayinsa na wakili na musamman na Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, wato ECOWAS, domin shiga tsakani da kawo sulhu a rikicin Mali.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan