Muddin ana son talaka ya sha jar miya sai an rage kuɗin da ake kashewa ƴan majalisu – Nasiru Zango

290

Fitaccen ɗan jaridar da ke aiki da gidan rediyon Freedom da ke jihar Kano, Nasiru Salisu Zango, ya ƙalubalanci yadda ake kashewa ƴan majalisun ƙasar nan maƙudan kuɗaɗe.

Nasiru Zango ya yi wannan sukar ne cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na facebook a safiyar yau Laraba, inda ɗaruruwan al’ummar da ke bin sa su ka tofa albarkacin bakinsu.

“Ni a tawa guntuwar fahimtar idan gaskiya ake so, idan har ana son talaka ya samu sassauci, maimakon ƙarin farashin Mai da Wutar lantarki, da an rage kuɗin da ake kashewa ƴan majalisu, a rage kudin abincin fadar shugaban ƙasa, a rage yawan motocin aiki a yiwa tsofaffin garanbawul, ina ga idan aka yi haka watakila talaka ya sha jar miya”

“Amma yanzu sai dai Yaɗiya da Tafasa, da ma sun fi ƙara lafiya. Idan kuma na saɓa lamba a bani datacciyar” In ji Nasiru Zango.

Kalaman na Nasiru Zango na zuwa ne kwana ɗaya da gwamnatin tarayya ta sanar da ƙarin kuɗin wutar lantarki na sama da kaso 50 cikin 100 na abin da kowanne mai amfani da lantarki zai rinka biya a kasar nan.

Sai dai jim kaɗan da wannan sanarwa hukumar samar da hasken wutar lantarkin ta nemi kafofin watsa labarai da su janye rahotannin da suka buga cewa hukumar ta yi ƙarin kudin wuta da kashi hamsin cikin dari.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan