A ƙarshe Donald Trump ya amince ya miƙawa Joe Biden mulki

144

Majalisar dattijan Amurka ta gudanar da taron ta a wani lokaci da siyasar kasar ta fuskanci barazana, biyo bayan tarzoma da ta rikide zuwa bore, inda wasu daga cikin magoya bayan shugaban kasar mai barin gado Donald Trump suka kutsa kai cikin majalisar.

Bayan kazamar zanga-zangar hana taron yan majalisun dattijan Amurka a harabar majalisar dake birnin Washigton, ƴan Majalisun sun gudanar da taron inda suka ayyana Joe Biden a matsayin wanda ya lashe zaben kasar na ranar 3 ga watan Nuwamba shekarar 2020.


Yan Majalisu 306 suka amince da nasarar Joe Biden, yayinda bangaren yan adawa 232 suka nuna adawa a kai.


Donald Trump ya amince ya mika mulki ranar 20 ga watan Janairu 2021. Shugaban mai barin gado ya aike da sako da cewa zai ci gaba da yakin siyasa bayan saukar sa daga karagar mulkin kasar Amurka.

Kasashen Duniya sun yi ta mayar da martani tareda nuna rashin amincewar ga abinda suka kira yiwa dimokuradiyya karen tsaye.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan