Atiku Ya Ƙaryata Cewa An Yi Masa Riga-kafin COVID-19

129

Atiku Support Organisation, ASO, ƙungiya mai rajin kare takarar shugaban ƙasa ta Atiku Abubakar, ta ƙaryata cewa Atikun ya karɓi allurar riga-kafin COVID-19 ta kamfanin Pfizer a Haɗɗaɗɗiyar Daular Larabawa, UAE.

Wani ɗan Kwamitin Takarar Shugaban Ƙasa taa Atiku Abubakar, Abdulrasheed Uba Sharada ya yi wata wallafa ranar Talata a shafinsa na Twitter, inda ya nuna hotunan da Atiku yana karɓar riga-kafin a UAE.

Sai dai wata sanarwa da Mataimakin Director na ASO, Kan Sabbin Kafafen Watsa Labarai, Muhammad Sunusi Hassan ya fitar ta ce an ɗauki hotunan ne a hargitse a wani asibiti, ba a wajen riga-kafi ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan