Elon Musk ya zama attajirin da ya fi kowa kuɗi a faɗin duniya

130

Attajirin nan mai kamfanin ƙera motoci na Tesla, Elon Musk, ya zama attajirin da ya fi kowa kuɗi a faɗin duniya.

Arzikin ɗan kasuwar mai shekara 50 ya ƙaru daga dala biliyan 153.5 zuwa jumilla dala biliyan 188.5, wanda hakan ya sanya shiga gaban attajirin nan mai kamfanin Amazon wato Jeff Bezos da kimanin dalar Amurka biliyan 1.5 kamar yadda jaridar Bloomberg ta ruwaito.

Tun a cikin shekarar 2017 dai atttajiri Jeff Bezos ya ke riƙe da kambun attajirin da ya fi kowa kuɗi a faɗin duniya.

Idan za a iya tunawa dai a cikin shekarar 2020 dukiyar Musk ta ƙaru da dala biliyan 100.3, kuma babu wanda ya samu ƙaruwar dukiya kamar wannan a jerin masu kuɗin duniya guda 500 na jaridar ta Bloomberg.

An dai haifi Elon Musk a birnin Pretoria na ƙasar Afirka ta Kudu. Haka kuma tun yana yaro yake yawaita tunane-tunane na ƙirƙirar abubuwa, abin da ta kai har sai da iyayensa da likitoci suka nemi a duba lafiyar kunnensa sakamakon rashin sauraron abubuwa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan