COVID-19: ‘Yan Najeriya Sun Dawo Daga Rakiyar Hukumar NCDC

154

A lokacin da hukumomin Najeriya suka sanar da cewa an samu ɓullar cutar COVID-19 a ƙasar a watan Fabrairu, 2020, da yawan ‘yan kasar sun yadda da hukumomin bisa wannan sanarwa.

Hakan ne yasa Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kafa dokar hana zirga-zirga da ake kira “lockdown” a Turance, kuma ‘yan Najeriya da dama sun yi biyayya ga wannan doka, duk da cewa dokar ta cutar da su ta ɓangaren tattalin arziƙi, zamantakewa, ilimi da sauransu.

A lokacin dokar kullen, kasuwanni, tashoshin mota, makarantu da sauran wuraren taruwar jama’a duk sun kasance a rufe.

Bayan bada sanarwar ɓullar cutar da hukumomin Najeriya suka yi, sai Cibiyar Taƙaita Yaɗuwar Cutuka ta Najeriya, NCDC, ta fara fitar da alƙakuman waɗanda suka kamu da cutar a duk rana.

NCDC, wadda ba kowa ya san ta ba kafin wannan lokaci, ta ci gaba da fitar da alƙaluma a kullum na waɗanda take cewa sun kamu da cutar tun daga wancan lokaci har ya zuwa yanzu.

A farko, a duk lokacin da NCDC ta wallafa alƙaluman waɗanda ta ce sun kamu da cutar a shafukanta na Facebook, Twitter da sauransu, ‘yan Najeriya sukan yadda da ita, tare da nuna alhini bisa samun ƙaruwar waɗanda take cewa sun kamu.

‘Yan Najeriya ma’abota amfani da shafukan Facebook, Twitter da sauransu, sukan bayyana yaddarsu da cutar ne ta hanyar bayyana ra’ayoyinsu a ƙarƙashin alƙaluman da NCDC ke fitarwa a kullum.

Sai dai da tafiya ta yi nisa, ‘yan Najeriya sun dawo daga rakiyar NCDC, domin kuwa sun fahimci cewar alƙaluman da take fitarwar biri-boko ne kawai.

‘Yan Najeriya sun buƙaci hukumar ta riƙa nuna musu waɗanda take cewa sun kamu da cutar, domin kuwa hakan ne kawai zai sa su yadda.

Misali, a alƙaluman da hukumar ta fitar ranar Alhamis da daddare, ta ce jimillar mutane 1,565 ne suka kamu da cutar a faɗin Najeriya a wannan rana.

Ga irin ra’ayoyin da mutane suka bayyana a ƙarƙashin wannan wallafa.

Abdurrahman Yusuf cewa ya yi:

“Wannan NCDC tana da ban dariya, amma tsawar da za ta faɗa a kansu har yanzu tana sama tana zaɓalɓala”.

“Ba ma ganin gawarwakin”, in ji Selina Ewansiha.

Godstime Ezema ya ce: “Allah Ya sa kwarankwatsa ta duka NCDC”.

Abd Salam Nuruddeen Opeyemi ya ce: “Don Allah banda jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, FCT, shin muna da wasu ne, saboda ban san a ina wannan cibiyar take samun alƙaluman ba koyaushe, ƙila dai daga China suke kwafowa”.

Itz DE Prince Emmanuel cewa ya yi:
“Ba na son yin magana game da wannan abin, amma jahilcin da hukumar da ake kira NCDC take yi ya yi yawa. Najeriya tana hannun Ubangiji”.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan