Kyan Ɗa: Ko ya kamata Sanata Rabi’u Kwankwaso ya karɓi hakimcin Madobi?

  152

  Tun bayan rasuwar Makaman Ƙaraye Alhaji Musa Sale Kwankwaso, kuma hakimin Madobi, a cikin watan Disambar shekarar 2020 al’umma ke tambayar cewa ko ya kamata tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ɗora daga inda mahaifin na sa ya tsaya?

  Kamar yadda masu iya magana kan ce Kyan Ɗa Ya Gaji Mahaifinsa, wannan haka ya ke domin Sanata Kwankwaso yana daga cikin jerin manyan ƴaƴan marigayi Makaman Ƙaraye, Alhaji Musa Sale Kwankwaso. Haka kuma al’ummar masarautar Madobi za su yi matuƙar murna da farin ciki idan aka ce yau Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne sabon Hakimin Madobi.

  Al’umma za su yi matuƙar mamakin a ce wai Sanata Kwankwaso zai karɓi sarautar hakimcin da mahaifinsa ya ɗauki tsahon shekaru yana yi, to wannan ba abin mamaki ba ne musamman batun harkar gadon Sarauta a ƙasar Hausa, domin burin kowanne ɗan Sarki to shi ne ya zama Sarki. Misali mun ga yadda mai martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmad Muhammad Sani II ya gaji mahaifinsa duk da cewa a lokacin yana kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano.

  Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

  Wani misali na nan kurkusa shi ne yadda mu ka ga Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, Jakadan Najeriya a ƙasar Thailand ya dangwarar da muƙamin jakadancin da ya ke yi ya nemi sarautar Zazzau, kuma ya dace domin ya zama sabon Sarkin Zazzau. Hakazalika mun ga yadda tsohon gwamnan bankin ƙasar nan Malam Muhammad Sanusi II ya garzayo ya nemi sarautar Kano, duk da cewa a lokacin al’umma suna ganin farin jininsa a tsakankanin ƴan Najeriya da sanayyarsa a ƙasashen duniya za su iya ba shi damar samun tikitin takarar shugabancin Najeriya a jam’iyya APC.

  Sai dai wani abu da al’umma ke kallon Rabi’u Musa Kwankwaso shi Mutum ne jajirtacce, mai ra’ayin siyasar ƴan mazan jiya kamar irin su marigayi Malam Aminu Kano, wanda hakan ya sa ake ganin sun yi watsi da sarautar gargajiya, inda su ka rungumi harkar siyasa domin hidimtawa al’umma.

  Amma koma dai yaya ne ba zai zama abin mamaki ba a ce Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zama sabon Makaman Ƙaraye Hakimin Madobi, domin Burin Ɗan Sarki Ya Zama Sarki!

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan