Za A Yi Wa Gwamnonin Najeriya Riga-kafin COVID-19 A Talabijin Don Gamsar Da ‘Yan Ƙasa

141

Gwamnonin Najeriya 36 sun amince a yi musu riga-kafin COVID-19 kai tsaye a gidajen talabijin don hakan ya taimaka wajen samuwar karɓuwar riga-kafin a tsakanin ‘yan Najeriya.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ne ya sanar da haka ranar Juma’a a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na Fadar Gwamnatin Tarayya bayan wata ganawar sirri da ya yi da Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.

“Mu ma za mu so nuna wa ‘yan Najeriya cewa mun yi imanin riga-kafin za ta yi aiki.

“Kungiyar Gwamnonin ta kula da yadda aka yi riga-kafin shan Inna kuma mun samu gogewa sosai.

“Mun yi aiki da da Hukumar Bunƙasa Lafiya Matakin Farko da Ma’aikatar Lafiya ta Ƙasa.

“Za mu yi farin cikin yin aiki da Cibiyar Taƙaita Yaɗuwar Cututtuka ta Najeriya, NCDC, Kwamitin Yaƙi da COVID-19 Na Shugaban Ƙasa da kuma Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko, NPHCDA.

“Saboda haka za mu ja ragama a jihohinmu daban-daban”, a cewar Kayode, wanda shi ne Gwamnan jihar Ekiti.

A ranar Alhamis, Babban Daraktan NPHCDA, Faisal Shuaib ya ce Shugaban Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo da sauran shahararrun ‘yan Najeriya sun bayyana shirinsu na yadda a yi musu riga-kafin kai tsaye a gidajen talabijin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan