Idan ba tsoro ba Abdullahi Abbas ya je a yi masa gwaji shan ƙwaya – Muaz Magaji

354

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Mu’azu Magaji mai laƙabin ɗan Sarauniya ya ce idan ba tsoro ba shugaban riko na jami’iyyar APC a jihar Kano Abdullahi Abbas yaje ayi masa gwajin kwaya kamar sauran ƴan takara.

Mu’azu Magaji cikin wani rubutu da ya wallafa mai taken “sakon abin tausayi” Abdullahi Abbas ya taba shawartar gwamna Ganduje da ya gwada kwakwalen duk wadanda zai baiwa mukami a dukkan matakai.

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban jam’iyyar Abdullahi Abbas ya tsara yiwa dukkanin wadanda za su yi takarar a zaben kananan hukumomi da na kansila ayi musu gwajin kwaya.

Sai dai bayan gwajin ne kuma hukumar NDLEA ta fitar da cewa ta samu wasu da dama da ga cikin ‘yan takarar da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

“Nima kafin a bani mukami an gwadani kuma na ci jarrabawar, mun godewa Allah.

“Amma yau yaranka da ka kawo a matsayin yan takara angwada galibinsu an tarar ‘yan kwayane.

“Abinda ya rage maka shi ne kai ma kaje a yi maka gwajin kwayar, koda yake munsan ma wane irin sakamako ne zai fito.


Kano Focus

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan