Ma’aikatan jami’ar Bayero da ke Kano sun tsunduma yajin aiki

181

Gamayyar ƙungiyoyin ma’aikatan jami’o’in Najeriya da su ka haɗa da SSANU ta manyan ma’aikata da NASU ta ƙananan ma’aikata reshen jami’ar Bayero da ke Kano, sun tsunduma yajin aikin kwanaki uku.

Da ya ke jawabin dalilin da ya sa su ka fara yajin aikin a gurin zanga-zangar lumana da su ka gudanar, shugaban ƙungiyar SSANU reshen jami’ar Bayero, Dakta Haruna Aliyu ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya ta gaza cimma alƙawarin da su ka yi a tsakaninsu.

Dakta Haruna Aliyu ya ƙara da cewa ƙungiyoyin SSANU da NASU na da matsala da tsarin biyan albashi na bai ɗaya, domin kuwa an yankewa mambobin ƙungiyar albashinsu ba tare da wani cikakken bayani ba.

Mambobin Ƙungiyoyin SSANU da NASU ke nan a lokacin da su ke gudanar da zanga-zangar lumanaExif_JPEG_420

Haka kuma ya ce sakamakon rashin ƙwarewa a tsarin biyan albashi na IPPIS, ya janyo an yankewa mambobin ƙungiyar kaso arba’in cikin ɗari na albashinsu. Haka kuma ya koka a game da yadda gwamnatin tarayya ta gaza biyansu alawus – alawus ɗin su tare da kuma ariyas ɗin samun tsarin albashi.

Hakazalika, Dakta Haruna Aliyu, ya yi ƙorafin cewa har kawo yanzu gwamnati ta gaza biyan haƙƙin mambobinsu na kamma aiki.

A ƙarshen zanga-zangar shugabannin kungiyoyin sun bayyana cewa yajin aikin na kwanaki uku zai zama shi ne matakin tafiya na sai baba – ta – gani.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan