Shekara 55 da kisan gillar da aka yiwa Fira Ministan Najeriya na farko

180

Alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa, mutum ne mai haƙuri, ladabi da biyayya, son haɗin kai tare kuma da cikakken kishin ƙasa wanda ya yi faɗa da zalunci.

Haka kuma Abubakar Tafawa Ɓalewa mutum ne mai kunya, maras yawan magana da tsantseni da kuma gudun duniya.

Wanene Alhaji Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa?

An haifi Sir Abubakar Tafawa Balewa a garin Tafawa Balewa dake jihar Bauchi a Arewa maso Gabashin Najeriya a shekarar 1912.

Ya kasance mutum mai da’a da kuma asali kasancewar mahaifinsa ma’aikaci ne ga hakimin garin.

Yayi karatu a makarantar horon malamai ta Katsina daga ( 1928 zuwa 1933), sannan ya zamo malami, kuma shugaban makarantar Bauchi Middle School.

Yayi karatu a makarantar horas da malamai ta London daga ( 1945 zuwa 1946), inda ya samu shaidar malanta.

A lokacin yakin duniya na biyu ya nuna sha’awarsa ta shiga harkokin siyasa, inda ya kafa zauren tattaunawa na Bauchi Discussion Circle.

Sannan daga bisani ya shiga siyasar malamai inda aka zabe shi mataimakin shugaban kungiyar malaman Arewa.

A shekarar 1952 ya zamo ministan ayyuka na Najeriya, ministan sufuri a 1954, sannan ya zamo jagoran jam’iyyar NPC a majalisar wakilai ta kasa.

Ya zamo Fira Ministan farko na Najeriya bayan da kasar ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960.

Gudunmawar Da Ya Bayar Wajen Cigaban Najeriya

Gudunmawar da gwamnatin Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa ta bayar abu ne mai wahalar ƙididdigewa, kasantuwar ita ce ta kafa tubalin duk wani ci gaba da ake iya gani yau a wannan ƙasa.

Kafa jami’o’i Huɗu na Nijeriya; Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya; Jami’ar Obafemi Awolowo; Jami’ar Nijeriya Nsukka da kuma Makarantar Tsaro ta Ƙasa (NDA) wadda take a matsayin jami’ar sojojin Nijeriya.

Kafa Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Afirka mai suna Organization of African Unity (OAU).

A shekarar 1963: Sabunta Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

A shekara 1964: Samar da dokar bayar da lambobin yabo domin girmama ‘yan ƙasa da suka hidimtawa ƙasa.

Rasuwar Alhaji Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa

A ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966, kimanin shekaru 55 da su ka gabata wasu sojojin Nijeriya ‘yan ƙabilar Ibo suka sace Alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa tare da kashe shi a yunƙurin su na hamɓarar da gwamnatinsa tare da wasu manyan ‘Yan siya da kuma sojoji daga yankunan Yamma da kuma Arewacin Nijeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan