Tuni na yi watsi da karatun boko na rungumi sana’ar wanki da guga – Ɗalibin jami’ar Bayero

249

Abubakar Idris Bashir dalibi ne a jami’ar Bayero da ke nan Kano da ya ce shi kam yanzu sana’ar da ya runguma ta wanki da guga ta fiye masa zuwa makaranta.

Abubakar ya ce tunda kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki ya shiga wani hali, sai dai daga bisani ya nemawa kansa mafita da ya rungumi sana’a.

A wata tattauna da jaridar Kano Focus Abubakar dan shekara 20 da ke zaune a unguwar tukuntawa kum ya ke karanta Geography a jami’ar ta Bayero ya ce tunda dai an zabi a kassara Ilimi shi kuma ya zabi ya kama sana’a.

A don haka ne kuma ya zabi ya fara sana’ar wanki da guga domin tallafawa kansa.

Na bata lokaci kan boko

Abubakar ya ce ada can ya bata lokacinsa da dama akan zuwa makaranta ba kuma ta samar masa da ko kwabo.

Yace kafin tafiya yajin aikin kungiyar ASUU naira dari biyar wahalar samu take yi masa sabanin yanzu da yake iya samun naira dubu biyu a rana.

A cewarsa a wata guda yana iya samun naira dubu hamsin zuwa sama.

”Yanayin kasarne sai a hankali da na dogara da cewa idan nagama makaranta zan samu aikin gwamnati ko na kamfani, to sai naga ya kamata na farka don na nemi na kaina ba tare da na dogara ga gwamnati ko wani ba.

“Kuma yanzu karatun ma bashi da tabbas in ka fara baka san lokacin da za ka gama ba.

“Kuna cikin yi sai ace an rufe makarantu sannan basu damu da mu ‘ya’yan talakawa ba,” a cewar sa.

Abokaina na min isgili

Ya kuma ce bayan daya lura cewa babu ranar bude makarantu hakan tasa ya fara tunanin me yakamata yayi don dogara da kansa.

“Na fara ne da wankin abokanaina lokacin da nace su kawo kayansu ina wanki da guga, wasu basu dauka da gaske nake ba, wasu kuma sai suka rinka cewa bai dace nayi sana’ar ba a isgilance

“Duk da haka ban karaya ba, a yanzu kaga bana tambayar kowa ya taimakamin da sisin kwabo, hasalima ni nake taimakawa wasu sanan nasiyi duk abinda raina yake so,”

Sana’ar na rufamin asiri

Ya kara da cewa sana’ar ta rufa masa asiri domin koda an koma makaranta zai iya biyan kudin makaranta da kansa ba tare da ya nemi tallafi daga gurin wani ba.

Sai dai yace matukar aka koma makaranta a yanzu ba lallai ya dinga samun wanki da guga kamar yadda yake samu ba, kuma hakan zai rage masa samun kudi.

Ya ce koda ba a sauya ranar komawa makarantun ba to tabbas zai rinka raba kafane don kuwa ba zai maida hankali kacokan akan karatu ba kamar yadda yayi a baya.

“Bazan karar da lokaci na a karatun boko ba, bayan kuma idan na gama ba lallai na samu aikin yi ba, amma kaga da wannan sana’ar idan Allah yasa mata albarka to sai na rufawa kaina asiri,” a cewar sa.

Hakazalika yayi kira ga ‘yan uwansa matasa dasu koyi sana’o’in dogaro dakai duba da halin da ilimi ya shiga a kasar nan.

Kano Focus

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan