Buhari da Osibanjo za su kashe fiye da Naira biliyan 3 wajen abinci da tafiye -tafiye

160

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo za su kashe naira biliyan 3 da miliyan 4 wajen cin abinci da tafiye – tafiye, kamar yadda kasafin kudin shekarar 2021 ya nuna.

A yayin da shugaba Buhari ya amince da ware wa ofishinsa naira biliyan 2 da miliyan dari 6, ya amince a kashe wa ofishin mataimakinsa, Osinbajo naira miliyan dari 8 da dubu 73.

Kamar yadda yake a shekaru biyar da suka gabata, a wannan karon ma akasarin kudaden da aka kasafta wa ofisoshin shugaban kasar da mataimakinsa za su shiga jerin tafiye-tafiyen da aka tsara za su yi ne a cikin shekarar.

A shekarar 2019, tafiye – tafiye da abinci na shugaban kasa da mataimakinsa sun lakume naira biliyan 1 da rabi, a 2018 sun lakume naira biliyan 1 da rabi da dubu dari 2, 2017, bilyan 1 da dubu dari 4 da 5, sai 2016 da aka kashe naira biliyan 1 da dubu dari 4 da 3 wajen abinci da tafiye – tafiye a fadar shugaban kasa da mataimakinsa.

Tafiye –tafiye a fadar shugaban ƙasa dai za su laƙume naira biliyan N2.4 billion, wato taifye tafiye a cikin kasar nan za su ci naira miliyan dari 775.6, a yayin da na wajen kasar nan za su laƙume naira N1.7.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Ya kamata shugaba Muhammadu buhari kaji tsoran Allah ka duba halin d kasarmu Nigeria ta shiga Amma Kai b ta talakawa kake ba ta tafiye-tafiyenka d abinda zakaci kawai kake Koda yake akwai ranar kin dillanci

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan