Na yi murna da aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi cikin lafiya da kwanciyar hankali – Ibrahim Shekarau

218

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ya ji matuƙar farin ciki da jin dadi da aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Kano, cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana haka ne a shafinsa na facebook, kwana ɗaya da kammala zaɓen ƙananan hukumomi a jihar ta Kano.

Daga labaran duk da muka samu a fadin jihar Kano, an yi zaɓuka lami – lafiya babu wani rahoton tashin hankali da tarzoma. Wannan abin farin ciki ne garemu. Zaman lafiya shi ne ginshikin arziki mai dorewa da bunkasar al’umma”

Haka kuma Sanata Ibrahim Shekarau ya ƙara da cewa ya aike da fatan alkhairi ga zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan guda 44 hukumomin da aka zaɓa.

Na aika da sakon fatan alheri da murna ta wannan babban nasara da muka samu a jihar Kano ga gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da shugaban riƙon na jam’iyyar APC na jiha Alhaji Abdullahi Abbas” In ji Malam Ibrahim Shekarau

A jiya ne aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a 44 a jihar Kano, inda aka gudanar da zaɓen a runfunan zaɓe 8084 a ƙanaana hukumomi 44 na jihar Kano.

Sai dai kuma zaɓen na ƙananan hukumomi a jihar Kano bai samu fitowar jama’a ba, domin akwai rumfunan da ba a ma gudanar da zaɓen ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan