Ƙasar Canada za ta tallafawa ƙasar nan da Dala Miliyan 10 saboda tsaro

199

Kasar Canada zata baiwa Najeriya dala miliyan goma amatsayin tallafawa gwamnati wajen yaki da matsalolin tsaro.

Jakadan Canada mai rikon kwarya a Najeriya Nicholas Simard ne ya bayyana bayar da wannan tallafin a da ya ziyarci ministan ‘yan sandan kasar nan Muhammad Maigari Dingyadi a Abuja, inda ya jaddada bukatar inganta karfin jami’an’ yan sanda, da sauran abubuwa don rage tashin hankali da kasar ke fuskanta.

Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na Ma’aikatar Harkokin ’Yan sanda, Odutayo Oluseyi, a cikin wata sanarwa a karshen mako, ya ruwaito Simard yana cewa Najeriya kasa ce mai ci gaba ta fuskoki da dama, to amma rashin tsaro na neman zama babban kalubale ga ci gabanta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan