Kishi Kumallon Mata: Wata mata ta hallaka budurwar mijinta a Kano

179

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta bayyana cewa sun samu nasarar cafke wata mata da ake zargin ta hallaka budurwar mijinta, wacce ya rage saura mako ɗaya a yi bikinta.

Matar mai suna Suwaiba Shuaibu mai kimanin shekaru 20 ana zarginta da kashe budurwar ne mai kimanin shekaru mai suna A’isha Kabir, mai shekaru 17 ta hanyar saɓa mata wuƙa a cikin wani kango da ke ƙaramar hukumar Doguwa da ke jihar Kano.

Kakakin rundunar ƴan sanda na jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce tun farko wani mai suna Kabiru Jafaru ne ya kai musu rahoton ɓatan budurwar.

Abdullahi Haruna Kiyawa ya ƙara da cewa binciken farko da jami’an ƴan sanda su ka gabatar ya ba su damar cafke Suwaiba Shuaibu.

Ya ƙara da cewa Suwaiba Shuaibu ta kasance matar wani mutum ce mai suna Shuaibu Ali, wanda kuma shi ne zai auri yarinyar da ake zargin Suwaiba ta kasheta.

“A lokacin da mu ke bincike, wacce ake zargin ta bayyana cewa ta kirawo budurwa ta hanyar buga mata waya, inda ta yaudareta zuwa wani kangon gini da ke maƙwaftaka da gidan da ta ke, inda ta yi amfani da wata kakkaifar wuƙa ta saɓa mata a wuya da ƙirjinta da wasu sassan jikinsa” in ji Abdullhi Kiyawa

“Na kashe A’isha ne saboda tsanani kishin da na ke yi da ita akan yadda na ga mijina zai aureta” in ji Suwaiba Shuaibu.

Tuni dai jami’a tsaro su ka miƙa gawar A’isha zuwa babban asibitin ƙaramar hukumar Tudun Wada.

A ƙarshe Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce tuni kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, Habu Sani ya bayar da umarnin yin bincike akan al’amari, da zarar kuma an kammala za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kuliya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan