Home / Labarai / Fiye da sojojin Najeriya guda 100 ne za su ajiye aiki

Fiye da sojojin Najeriya guda 100 ne za su ajiye aiki

Adadin sojojin Najeriya guda 127 ne za su ajiye aikin soja duk kuwa da matsanancin matsalar tsaron da ake fuskanta a wasu sassan kasar nan.

Sojojin, sun fito ne daga bataliyoyi dabam dabam na sojin kasar, ba masu manyan mukami bane, kuma akasarin su na bakin daga a wuraren da ake samun matsalolin tsaro.

Jami’an sojin da suka hada da mai mukamin Master Warrant Officer guda, Warrant Officer 3, Staff Sergent 22, sergent 29, Corporal 64, sai masu mukamin Lance Corporal da Private 7 za su yi ban kwana da aikin soja ne a watan Mayun wannan shekarar, kamar yadda kamar yadda wata sanarwa daga shelkwatar sojin ta kunsa.

Kuma rahotanni na cewa tuni babban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Tukur Buratai ya amince da barin aikin na su.

Sai dai sanarwar da ke dauke da sunayen sojojin da za su ajiye aikin ba ta banbanta tsakanin wadanda ke barin aiki don ra’ayin kansu, da kuma wadanda ke bari don dalilai na rashin lafiya ba.

Wata sanarwar da wani Birgediya Janar T.A Gagariga, ya sanya wa hannu ta umurci sojojin 127 masu niyyar murabus da su mika duk wani abu na soji da ke tare da su

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Yadda aka yi addu’ar cikar Sarkin Rano Kabiru Muhammad Inuwa shekara 1 a kan mulki

Sarkin Rano Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa, ya jagoranci addu’a ta musamman domin murnar cikarsa shekara …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *