Alwaleed Bin Talal: Hamshaƙin Attajiri Musulmi Mai Kyautar Ban Mamaki

202

A ranar 7 ga Maris 1955, aka haifi shahararren attajirin nan ɗan ƙasar Saudiyya, Al-Walid bn Talal bn Abdul-Aziz Al-Saud. Al-Walid, wanda ya fito daga gidan Sarautar Saudiyya, ya shahara a duniya saboda ɗimbin dukiya da Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba shi, da yadda yake ciyar da dukiyar wajen taimakon alumma.

An haifi Talal a garin Jidda. Ya yi digirinsa na farko a Harkar Kasuwanci, wato Business Administration a Kwalejin Menlo dake Califonia a shekarar 1979, sannan ya yi Digirinsa na Biyu a Harkar Zamantakewa, wato Social Science a Jamiar Syrawse dake New York a Amurka a 1985. (http://www.forbes.com/profile/prince-alawleed-bintalal-al-saud).

Al-Walid ya fara kasuwancinsa a shekarar 1979 bayan ya ƙare digirinsa na farko, inda ya sanya kuɗi masu yawa a shahararren kamfanin nan na Citigroup dake Amurka, wanda ya sanya shi zama mutum mafi kuɗi a yankin Larabawa. A shekarar 1987, mujallar Times ta ce, shi ke da jarin kashi 5% a shahararren kamfanin Yaɗa Labarai na Amurka New Corporation’. A shekarar 2010 ya kai kashi 7% wanda kuɗinsa suka kai dala biliyan $3, haka kuma yana da kimanin dala miliyan $70, kimanin kashi tara (9%) a kamfanin Rotane Group kamfanin hada-hada na labarai mafi girma a duniya. (News Corp. The Saudi Prince And The Ground Zero Mosque. Sam Gustin. Daily Financial).

A 1999, mujallar tattalin arziƙi ta Amurka ta yi mamakin inda yake samun kuɗi ta yadda kasuwancinsa ke bunƙasa kamar gobarar daji. (The Mystery Of The Worlds Second-richest Business. The Economist. 25-02-1999).
Haka nan, Al-Walid ya sanya maƙudan kuɗaɗe a kamfanin ACL, APPLE Inc., MCI Inc., Motorola, Fox News da sauransu. Haka kuma, Al-Walid yana da maƙudan kuɗaɗe a manyan otal-otal a Turai. (Disneyland Resort Paris, Annual Review 2007, Shafi Na 53.

A shekarar 2009, an ruwaito cewa Al-Walid ne yake da kashi 30% na jari a kamfanin Saudi Research And Marketing Group, kamfanin yaɗa labarai mafi girma a Gabas Ta Tsakiya. (Ideological And Ownership Trends In the Saudi Media. Cable Gate. 11 May, 2009).

Haka dai Al-Walid yana da kudi a wasu manyan kamfanoni da cibiyoyin ciniki masu girma a duniya wanda ba za a iya kawowa a nan ba. Al-Walid shi ke da shahararren kamfanin nan na Kingdom Holding Company, wanda kana iya cewa gamayyar kamfanoninsa ne na kasuwanci, wanda a watan Agusta 2011 ya bayyana aniyarsa ta gina Kingdom Tower, gini mafi girma da tsawo a duniya da aka ƙiyasta zai ci dala biliyan $1.23 a Saudiyya. (Saudi Plan World Tallest Tower, Sumner Said. 13 August 2011).

Amfanin arziƙi shi ne ciyar da dukiyar wajen ayyukan alheri, Al-Walid ya narka maƙudan kuɗaɗe wajen taimaka wa alumma a ɓangarori masu yawa a duniya.

An ce mafi yawan ayyukansa na alheri ya fi karkata su zuwa harkar ilmi domin ƙoƙarin cike giɓi tsakanin ilimin Musulunci da na Turawa. Ya sanya kuɗi a manyan jamioi da cibiyoyin ilimi a Amurka da Gabas Ta Tsakiya.

A harin 11/9 da aka kai wa Amurka, ya ba wa Amurkar gudunmawar dala miliyan $10,, daga baya ya janye. (Al-Ahran Weekly, Big Bad Apple. 18-24-October, 2001).

A shekarar 2002 a lokacin wani hari da Yahudawa suka kai wa Musulmin Falasɗinu a West Bank, Al-Walid ya ba wa Musulmin Falasɗinun gudunmawar dala miliyan $18.5, wannan kuwa sakamakon kiran da Sarki Fahad ɗan Abdul-Aziz ya yi ne na a taimaka musu, wanda Saudiyya ta haɗa gudunmawar kimanin dala miliyan $77, (Saudi Telethon Raises &77 Million. CNN 7 January, 2005).

Haka kuma a 2002, Al-Walid ya bada gudunmawar dala miliyan $500,000 ga Gidauniyar George Bush don ba da gudunmawar karatu (scholarship) ga Makarantar Philliphs Academy dake garin Andover. (News Corp. The Saudi Prince And The Ground Zero Mosque. Sam Gustin. Daily Financial).

Haka kuma a shekarar 2004, yayin ambaliyar Tsunami da ta faru, Al-Walid ya bada gudunmawar dala miliyan $17. A shekarar 2008, ya bada gudunmawar dala miliyan $8 don gina Cibiyar Koyar Da Ilimin Addinin Musulunci da aka sanya mata sunansa a Jamiar Cambridge dake London. (Arab And Islamic Funding Of Islamic Studies: A Question Of Western Security. Glees Anthony (2009).

Watanni kaɗan bayan haka, ya bada dala miliyan $16 ga Jamiar Edinburgh ita ma don gina Sashen Addinin Musulunci. (Saudi Prince Donates $16m To Improve Islamic Studies. Times Higher Education. 8 May, 2008).

Haka kuma, a Afrilun 2009, ya ba wa Jamiar Harvard dala miliyan $20, wafda ta zama cikin gudunmawa mafi girma da ta taɓa Jamiar ta samu tun daga kafa ta. Ya bada irin wannan gudunmawar (dala miliyan $20) ga Jamiar Goege Town, (Arab And Islamic Funding Of Islamic Studies: A Question of Western Security. Glees Anthony (2009).

Akwai gudunmawa da tallafi da ya bayar iri-iri daban-daban da ba za su iya faɗuwa ba. Wannan ta sa ya zama shahararren mutum a duniyar wannan lokaci, kuma ya sami kyautukan girmamawa masu yawa a duniya da suka hadar da kyautar; Dwight D. Eisenhowar a 2010, da kyautar Sarkin Bahrain mafi girma ta Bahrain Medal of the First Order a Mayun 2012 da sauransu.

Aliyu Ibrabim Sani Mainagge malami ne, marubuci kuma manazarci.
Ya rubuto daga Kano.
Za a iya samun sa a kan lambar waya: 08068985599, ko adireshin imel:alibabapress2020@gmail.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan