Kotu Ta Bada Umarnin Ƙwace Kuɗaɗen Tsohon Gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari

100

A ranar Talatar nan ne Babbar Kotun Tarayya, Abuja, ta bada umarnin ƙwace kuɗaɗen tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, da suke ajiye a asusan Bankunan Zenith da Polaris.

Kuɗaɗen sun haɗa da dalar Amurka dubu $56,056.75 a Polaris Bank; miliyan N12.9, miliyan N11.2, dala $301,319.99; N217,388.04 da dala $311,872.15 a asusan Bankin Zenith daban-daban da aka ajiye da sunan Yari da kamfanoninsa.

Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu, a wani hukunci da ya yanke, ya tabbatar da cewa tsohon Gwamnan bai bada ƙwaƙƙwaran dalili da zai hana Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Da Dangoginsa, ICPC, ba za ta bincike shi ba.

ICPC ta shigar da ƙara ne a kotun, inda take roƙon kotun ta sa Gwamnan ya yi jawabin abin da zai hana a mayar da kuɗaɗen zuwa ga asusun gwamnatin tarayya ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya bada rahoton cewa yayin da Yari yake a matsayin wanda ake ƙara na farko a ƙarar mai lamba: FHC/ABJ/CS/916/2019, kamfanoninsa biyu, Kayatawa Nigeria Limited da B. T. Oil da Gas Nigeria Limited, su ne waɗanda ake ƙara na biyu da na uku.

A ranar 16 ga Agusta, 2019, Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya bada umarnin ƙwace kuɗaɗen na wucin gadi a ƙarar da lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha.

ICPC ta yi zargin cewa kuɗaɗen ba a same su ta hanyar da ta dace ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan