Ko Kun San Atiku Ba Ya Zama A Najeriya Sai Lokacin Zaɓe Ya Yi?

448

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, yana ɗaya daga cikin ‘yan kasuwa kuma ‘yan siyasa da suka fi kowa yin nasara a Najeriya. Amma har yanzu buƙatar zama Shugaban Najeriya ce ta fi damun sa, kuma yana yin dukkan mai yiwuwa don cim ma haka.

Duk da dai harkokin kasuwancinsa suna Najeriya ne, bisa dalilan da shi kaɗai ya sani, amma dai ya fi jin daɗin zama a Dubai. Jaridar Social Circuit ta gano cewa tun lokacin da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a 2019 ya kayar da shi a zaɓe ya koma Dubai da zama.

Mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, Deji Adeyanju, ya tabbatar da haka, inda yake tambayar Atiku me yasa ya zaɓi zama a ƙasashen ƙetare, san nan ba ya dawo wa Najeriya sai lokacin zaɓe ya yi.

Ya ce: “Atiku ya shafe fiye da shekara biyu a Dubai tun lokacin da ya sha kaye a zaɓen da ya gabata. Ya zo bikin ‘ya’yansa ya koma. Zai dawo a 2023 ya ce yana son zama Shugaban Ƙasa. Me yasa ba zai tsaya takarar wani muƙami ba a Dubai”?.

Bayan ya yi aiki a Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Najeriya, NCS, na tsawon shekaru 20, inda har ya zama Mataimakin Darakta, ya bar aiki ya shiga kasuwanci da siyasa gadan-gadan.

Ya fara hada-hadar gidaje a lokacin da yake aiki a NCS, kafin ya shiga ɓangaren aikin gona, shigo da kayayyaki, harkar sadarwa da kamfanonin kayan zaƙi da harkar ilimi.

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Rashin Zama a Najeriya Shine rashin taimaka wa jama’a koko yaya?

    Yan zukuma tanan akabullo dan 6atanci ga mai girma ALH. Atiku Abubakar Tom, 2023 tashi ne da izinin Allaah

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan