Wani alƙali ya yankewa wasu matasa ɗaurin shekara 30 a gidan yari kan shan tabar wiwi

193

Wasu rahotani daga ƙasar Tunisia sun ce an yanke wa wasu matasa uku hukuncin daurin shekara 30 a gidan kaso bayan da aka kama su suna shan tabar wiwi a filin wasan kwallon kafa.

Kakakin kotun da ta yanke hukuncin ya ce an same su da laifi karya wasu dokoki uku da ba su da alaka da juna, da suka hada dokar data nemi a yanke hukuncin dauri shekara goma akan masu ta’amali da miyagun kwayoyi da kuma dokar data nemi shekara 20 a kan shan miyagun kwayoyi a bainar jama’a.

Sai dai wani dan majalisa ya nemi shugaban kasa ya yi musu ahuwa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan