Al’ajabi: Ciwo ya fi warkewa da wuri a duniyar sama

235

Wani ɗan sama jannati ɗan kasar Rasha, mai suna Sergey Kud-Sverchkov ya bayyana cewa, ciwo ya fi warkewa a duniyar sama.

Kamfanin dillancin labarai na Sputnik ya bayyana sanarwar da Sergey Kud-Sverchkov da ke aiki a tashar ‘yan sama jannati ta kasa da kasa ya fitar ta shafinsa na Twitter.

A sanarwar Sergey Kud-Sverchkov ya ce “A wajena, ciwo ya fi warkewa a duniyar sama. Watakila dalilin hakan shi ne yadda babu kwayoyin cuta da yawa a sama, kuma ana da iska busasshiya.”

A tashar ƴan sama jannati ta kasa da kasa akwai ‘yan kasar Rasha Sergey Kud-Sverchkov da Sergey Rikikov da kuma Amurkawa Kate Rubins, Michael Hopkins, Victor Glover da Shannon Walke sai kuma dan kasar Japan Soichi Noguchi da ke gudanar da aiyukan bincike.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan