Duk wanda ya ke son aiki da gwamnatin Kano dole sai ya shiga jam’iyyar APC – Abdullahi Abbs

433

Shugaban riƙo na jam’iyyar APC a jihar Kano Abdullahi Abbas ya buƙaci gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da ka da ya kuskura ya ɗauki kowa aikin gwamnati har sai ya shiga jam’iyyar APC.

Haka kuma ya gargadi ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da sauran masu amfana da gwamnatin Ganduje da su shiga jam’iyyar APC ko kuma a janye mu su dukkanin wata dama da suke samu a gwamnatin.

Abdullahi Abbas na wanna barazana ne a lokacin ƙaddamar da fara rjistar zama ɗan jam’iyyar APC a jihar Kano da aka gudanar a jiya Litinin.

Ya ce gwamnatin Kano ba za ta lamunci duk wani da ke aiki a ƙarƙashinta ba kuma ba shi da katin zama ɗan jam’iyyar APC.

A don hakan ne ma ya bukaci dukkanin ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da ofisoshin siyasa a fadin jihar Kano, su tabbatar sun mallaki katin zama mamba a jam’iyyar APC.

Ya kuma ce ba wai su kaɗai umarnin ya shafa ba, ya zama dole su fito da iyalansu da ma duk wadanda suke da iko da su baki ɗaya domin yin rijstar.

“Muna buƙatar mu tashi tsaye, mu tabbatar mun samu nasarar yin rijistar mambobi da yawa a jam’iyyarmu ta APC

“Dukkan masu riƙe da ofisoshin siyasa, dukkanin ma’aikatan gwamnati, da dukan wanda ke kowanne irin aiki ne a ƙarƙashin gwamnatin Kano, ya zama dole su fito su yi rijista da jam’iyyar APC.

“Ba ma su kaɗai ba, harma da duk danginsu da abokansu da sauran waɗanda suka isa da su, su sanya su su yi rijista da jam’iyyar APC

“Ina kira ga gwamnan Kano da ka da ya sake baiwa kowa aikin gwamnati har sai yana da katin jam’iyyar APC” a cewar Abdullahi Abbas

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan