Jami’ar Bayero da ke Kano ta ƙaddamar da gangamin yaƙi da satar amsa

179

Ɗaliban sashen harkokin yaɗa labarai da Ilimin aikin jarida a jami’ar Bayero da ke Kano, sun ƙaddamar da wani gangami akan yaƙi da satar amsa a tsakankanin ɗalibai domin kawo ƙarshen matsalar satar amsa.

Ɗaliban sun ƙaddamar da Gangamin mai taken #BUKSayNo2ExamsMalpractice, a jiya Litinin 1 ga watan Fabrairu.

Tun da farko babban maƙusidin ƙaddamar da gangamin shi ne faɗakar da ɗalibai tare Ilimantar da su illolin satar amsa tare kuma da ƙarfafa musu gwiwa akan zage damtse wajen yin karatu tare da mayar da hankali akan karatun da ake koya musu.

Haka kuma za a yayata gangamin a shafukan WhatsApp da Facebook da Instagram da kuma Twitter, a tsakankanin ɗaliban jami’ar.

Jagoran gangamin, Rabi’u Musa ya ce sun ƙirƙiro gangamin ne domin kawo ƙarshen matsalar satar amsa a tsakankanin ɗalibai, wanda ya zama ruwan dare a makarantun Sakandare da kuma manyan makarantu a faɗin ƙasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan