Home / Ilimi / Buhari Ya Amince Da Buɗe Sabbin Jami’o’i 20 A Najeriya

Buhari Ya Amince Da Buɗe Sabbin Jami’o’i 20 A Najeriya

Majalisar Zartarwa ta Najeriya, FEC, ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu har guda 20 a faɗin Najeriya.

A ranar Larabar nan ne FEC ta amince da kafa sabbin jami’o’in a yayin taronta na tattaunawa da take yi duk mako.

Wannan amincewar kuma ta biyo bayan wata takarda da Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya gabatar a yayin taron tattaunawar na FEC, wanda Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Tara daga cikin waɗannan jami’o’i masu zaman kansu suna Arewa ta Tsakiya ne, uku suna Kudu Maso Kudu, biyu a Kudu Maso Gabas, biyar a Arewa Maso Yamma, sai ɗaya a Kudu Maso Yamma.

Da yake yi wa manema labarai jawabi jim kaɗan bayan kammala taron, Ministan ya ce jami’in da aka amince a buɗe ɗin za su samu lasisi na wucin gadi daga Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya, NUC.

Ya ce jami’o’in su ne Jami’ar Topfaith Mkpatak, Jihar Akwa Ibom; Jami’ar Thomas Adewumi, Oko-Irese, Jihar Kwara; Jami’ar Maranathan, Mgbidi, Jihar Imo; Jami’ar Ave Maria, Piyanko, Jihar Nasarawa da Jami’ar Al-Istiqama, Sumaila, Jihar Kano.

Akwai kuma Jami’ar Mudiame, Irrua, Jihar; Jami’ar Havilla, Nde-Ikom, Jihar Kuros River; Jami’ar Claretian ta Najeriya, Nekede, Jihar Imo; Jami’ar NOK, Kachia, Jihar Kaduna da Jami’ar Karl-Kumm University, Vom, Jihar Filato.

Sai kuma Jami’ar James Hope University, Legas, Jihar Legas; Maryam Abacha American University of Nigeria, Kano, Jihar Kano; Jami’ar Capital City, Kano, Jihar Kan; Jami’ar Ahman Pategi, Pategi, Jihar Kwara, da Jami’ar Offa, Offa, Jihar Kwara.

Sauran Jami’ar Mewar, Masaka, Jihar Nasarawa, Jami’ar Edusoko, Bida, Jihar Neja; Jami’ar Philomath, Kuje, Abuja; Jami’ar Khadija, Majia, Jihar Jigawa da Jami’ar Anan, Kwall, Jihar Filato.

About Hassan Hamza

Check Also

Bayyanar Shehu Da Bayanan Kariya a Jihar Borno

Ƙungiyar Translators Without Boarders (TWB), ta kirkiro wata manhaja da aka yi wa lakabi da 'Shehu'. Ta hanyar amfani da wannan manhaja, za a iya samun dukkanin sahihan bayanai da suka shafi cutar Korona ko rigakafinta. Bayanan, sun hada da yadda ake kamuwa da cutar, yadda za a tsaftace kai da muhalli, tare da kuma kahanyoyin kare kai daga ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *