Home / Ilimi / Buhari Ya Amince Da Buɗe Sabbin Jami’o’i 20 A Najeriya

Buhari Ya Amince Da Buɗe Sabbin Jami’o’i 20 A Najeriya

Majalisar Zartarwa ta Najeriya, FEC, ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu har guda 20 a faɗin Najeriya.

A ranar Larabar nan ne FEC ta amince da kafa sabbin jami’o’in a yayin taronta na tattaunawa da take yi duk mako.

Wannan amincewar kuma ta biyo bayan wata takarda da Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya gabatar a yayin taron tattaunawar na FEC, wanda Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Tara daga cikin waɗannan jami’o’i masu zaman kansu suna Arewa ta Tsakiya ne, uku suna Kudu Maso Kudu, biyu a Kudu Maso Gabas, biyar a Arewa Maso Yamma, sai ɗaya a Kudu Maso Yamma.

Da yake yi wa manema labarai jawabi jim kaɗan bayan kammala taron, Ministan ya ce jami’in da aka amince a buɗe ɗin za su samu lasisi na wucin gadi daga Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya, NUC.

Ya ce jami’o’in su ne Jami’ar Topfaith Mkpatak, Jihar Akwa Ibom; Jami’ar Thomas Adewumi, Oko-Irese, Jihar Kwara; Jami’ar Maranathan, Mgbidi, Jihar Imo; Jami’ar Ave Maria, Piyanko, Jihar Nasarawa da Jami’ar Al-Istiqama, Sumaila, Jihar Kano.

Akwai kuma Jami’ar Mudiame, Irrua, Jihar; Jami’ar Havilla, Nde-Ikom, Jihar Kuros River; Jami’ar Claretian ta Najeriya, Nekede, Jihar Imo; Jami’ar NOK, Kachia, Jihar Kaduna da Jami’ar Karl-Kumm University, Vom, Jihar Filato.

Sai kuma Jami’ar James Hope University, Legas, Jihar Legas; Maryam Abacha American University of Nigeria, Kano, Jihar Kano; Jami’ar Capital City, Kano, Jihar Kan; Jami’ar Ahman Pategi, Pategi, Jihar Kwara, da Jami’ar Offa, Offa, Jihar Kwara.

Sauran Jami’ar Mewar, Masaka, Jihar Nasarawa, Jami’ar Edusoko, Bida, Jihar Neja; Jami’ar Philomath, Kuje, Abuja; Jami’ar Khadija, Majia, Jihar Jigawa da Jami’ar Anan, Kwall, Jihar Filato.

About Hassan Hamza

Check Also

Mun Buɗe Cibiyoyin Rijista Na Bogi Don Mu Kama Masu Satar Jarrabawa— JAMB

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandare, JAMB, ta kafa abin da ta …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *