Home / Labarai / Rashin wutar lantarki ya sanya an cire Najeriya daga ƙasashen da za su karɓi tallafin rigakafin Korona

Rashin wutar lantarki ya sanya an cire Najeriya daga ƙasashen da za su karɓi tallafin rigakafin Korona

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta cire sunan Najeriya daga cikin jerin kasashen Afirka da zasu karbi allurar rigakafin cutar korona daga kamfanin Pfizer-BioNTech a karshen wannan wata saboda rashin samar da wuri mai sanyi da ake bukata na aje magungunan.

Daraktar Hukumar dake kula da kasashen Afirka Matshidiso Moeti, tace an dauki matakin ne saboda rashin samar da wuraren dake da sanyi kasa da maki 70 domin kare ingancin maganin.

Matakin WHO na zuwa ne a yayin da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya Kayode Fayemi ya ce suna aiki da Bankin Duniya domin ganin an samarwa kasar nan maganin rigakafin.

Fayemi yace Najeriya na daya daga cikin kasashe 12 daga Afirka da suka bayyana aniyar su ta samar da inda za’a aje maganin kafin karshen wannan wata na Fabarairu, sai dai Moeti yace kasashen Afirka 4 kacal suka samar da wuraren da ake bukata wadanda suka hada da Cape Verde da Rwanda da Afirka ta Kudu da kuma Tunisia.

Hukumar yaki da cututtuka tace mutane sama da 138,000 suka harbu da cutar a Najeriya, kuma 1,640 daga cikin su sun mutu.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *