Home / Addini / Rashin gina alƙaryar shirya fina-finai a Kano babbar asara ce – Sani Lawan Malumfashi

Rashin gina alƙaryar shirya fina-finai a Kano babbar asara ce – Sani Lawan Malumfashi

Tsohon shugaban hukumar zaɓe ta jihar Kano KANSIEC kuma malami a sashen nazarin halayyar ɗan adam a jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ya bayyana cewa rashin gina alƙaryar shirya fina – finai a jihar Kano (Film Village) babbar asara ce ga cigaban jihar.

Farfesa Sani Lawan Malumfashi ya bayyana hakan ne a lokacin a ɗaya daga cikin shirye-shiryen da ake gabatarwa a wani gidan rediyo mai zaman kan sa da ke Kano. Ya ce gina alƙaryar shirin fina -finan zai samar da ɗimbin ayyukan yi ga matasan jihar ta Kano.

Farfesan ya ce tun daga kan mai shirya wasan kwaikwayon da kuma sauran jaruman har zuwa kan masu ɗaukar hoto a masana’antar Kanywood za su sami aikin yi wanda hakan zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin jihar Kano.

Farfesa Sani Lawan Malumfashi

Haka kuma Farfesan ya ce ita kan ta jihar Kano za ta samu ƙarin kuɗin shiga tare da ingantuwar tsaro la’akari da yadda za a samu masaukin kwana daban – daban a gurin, wanda hakan zai sanya baƙi daga ƙasashen Amurka da Turai su dinga kawo ziyara ta musamman.

Hakazalika Sani Lawan ya ƙara da cewa da a ce an samar da alƙaryar shirya fina-finai a jihar Kano, to babu shakka za a samu masu shirya fina – finai daga ƙasashen Indiya da Amurka da za su zo su ɗauki shirin fim a jihar Kano.

Idan za a iya tunawa dai a cikin shekarar 2016 ne gwamnatin tarayyar da hadin guiwar gwamnatin jihar Kano su ka shirya samar da wani katafaren alƙaryar shirya fina finai a jihar Kano, wato Film Village a garin Kofa dake karamar hukumar Bebeji wanda shirin ya gamu da tangarɗa.

Haka kuma da a ce an samar da alƙaryar ɗin za ta kasance ta farko a Najeriya, kuma ta biyu a nahiyar Afirka.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Sheikh Ɗahiru Bauchi Zai Jagoranci Sallar Idi Ranar Laraba

Fitaccen malamin addinin Musluncin nan a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Bauchi zai jagoranci Sallar Idin Ƙaramar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *