Ɗan Ɗahiru Mangal Ya Rasu Sakamakon Mummunan Haɗarin Babur

121

Nura Ɗahiru Mangal, ɗa ga hamsaƙin attajirin nan na jihar Katsina, Alhaji Ɗahiru Mangal, ya rasu a wani mummunan haɗari da ya rutsa da shi a kan babur ɗin tsere.

Wata majiya dake da kudanci da iyalan Alhaji Mangal ta shaida wa jaridar Intanet mai bada labaran Katsina zalla, Katsina Post, cewa marigayin ya rasu ne sakamakon haɗari da ya yi a kan babur na tsere a kan Titin Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a ranar Laraba.

Za yi jana’izar sa a gobe da misalin ƙarfe 10:00 na safe.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan