Cocin Cherubim da Seraphim Movement Church Worldwide, jihar Kwara ta haramta wa mata amfani da hijabi a Kwalejin Cherubim da Seraphim, llori.
A kwanan nan ne dai gwamnatin jihar Kwara ta kafa dokar amfani da hijabi a dukkan makarantun gwamnati.
Jagoran Cocin, Most Reverend Samuel Abidoye, ya sanar da haka ga manema labarai ranar Lahadi a babban birnin jihar Kwara, Ilori.
A cewarsa, cocin ba ta yadda ɗalibai mata na kwalejin su yi amfani da hijabin Musulmi ba.
Ya ce cocin ita take da alhakin tafiyar da makarantar, da kuma sa doka bisa irin kayan da ya kamata a riƙa sawa.
Sakataren Lardin Ilori na Cherubim da Seraphim da kuma Cocin, Samson Ibidoja, ya jaddada cewa da ma can cocin ce kaɗai ke tafiyar da makarantar.
Ya ce Kwalejin Cherubim da Seraphim, Sabo-oke, llori, mallakin Seraphim Church Worldwide, an kafa ta ne a 1969 don kula da ci gaban ilimin yara.
Saboda haka ne sai cocin ta shawarci gwamnatin jihar da ta sake duba hukuncinta don kauce wa tashin hankali da karyewar doka da oda a jihar.
Da yake mayar da martani, Shugaban Musulmi Masu Ruwa da Tsaki a Kwara, Farfesa Hamzat AbdulRaheem, ya ce ya zama wajibi dukkan makarantu su girmama dokar saka hijabi da gwamnatin jihar ta kafa don a samu zaman lafiya.
“Abin da ‘yan uwa Kirista suke nuna wa duniya ƙarya ce, akwai makarantun Kiristoci masu zaman kansu da yawa a jihar nan waɗanda Musulmi ba za su iya tilasta dokar saka hijabi ba, amma a makarantun gwamnati daban ne”, in ji shi.
Ya ce Kwalejin Cherubim da Seraphim, kamar wasu makarantu da wasu ƙungiyoyin Musulmi suka kafa, ba wai mallakin ƙungiyoyin Mishin ba ne kaɗai, saboda haka ba su ne za su ce ga yadda za a gudanar da makarantun ba.
Farfesa AbdulRaheem ya shawarci Cocin Cherubim da Seraphim da ko dai ta bi dokar gwamnatin jihar ta amfani da hijabi, ko kuma ta buƙaci a ba ta izinin kula da makarantar.
Kimanin makarantun Kiristoci 10 gwamnatin jihar kwara ta rufe sakamakon haramta amfani da hijabi da suka yi, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito.
Bayan haka ne sai gwamnatin jihar ta kira taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki tsakanin Kiristoci da Musulmi, ta kuma kafa dokar amfani da hijabi.