Ko Alarammomi Masu Almajirai Su Bar Kaduna Ko In Kore Su— El-Rufai’i

132

Nasir El-Rufai, Gwamnan jihar Kaduna, ya buƙaci masu makarantun almajirai da su tashi su bar jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Talata a yayin ƙaddamar da Kwamitin Jin Daɗi da Kare Haƙƙin Yara na Jihar Kaduna.

“Muna aiki a kan tsarin almajiranci amma mutane da yawa ba su yadda da abin da muke yi ba, amma muna da ƙwarin guiwa da kuma tabbacin cewa abin da muke yi daidai ne.

“Saboda haka, saƙona ga masu almajirai a jihar Kaduna, kuna da zaɓi ku koma wasu wuraren ko kuma mu kore ku ko yanzu ko nan gaba”, in ji Gwamna El-Rufai’i.

Ya ce gwamnati ta samar tare da amincewa da tsarin walwalar jama’a.

Ya ce an yi haka ne don a samu dokoki da za a taimaka wa talakawa da marasa galihu.

“Muna son mutane mafiya talauci su amfana. Yawanci ‘yan siyasa sukan zo da tunaninsu na a ba su guraben aiki, kuma idan muka ba su guraben aikin ba sa ba mutane mafiya talauci.

“To dole mu samu wata hanya don gano wane ne talaka kuma wane ne mara galihu don mu kai irin wannan taimakon ga irin waɗannan iyalai”, ya ƙara da haka.

Gwamna El-Rufai’i ya ce Ofishin Kula da Walwalar Jama’a na Jihar yana aiki a dukkan ƙananan hukumomi 24 na jihar don samun cikakkiyar rijistar kula da walwalar mutane marasa galihu.

Ya ƙara da cewa rijistar kula da walwalar tana da mutane fiye da miliyan ɗaya, ya kuma tabbatar da cewa duk wani tallafin gwamnati zai riƙa zuwa ga mabuƙata kai tsaye.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan