Andawo da Tashi da Saukar Jiragen Saman Ƙasa da Ƙasa a Jihar Kano

223

An dawo da tashi da sauka na jiragen saman ƙasa da ƙasa a filin tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano a yau Talata 6 ga Afrilu, 2021, inda jirgin farko ya taso daga ADIS ABABA dake Ƙasar Ethiopia kuma ya sauka a jihar Kano.

Hukumomin sauka da tashin jirage da hukomomin Lafiya na jihar Kano sun sanya sharuddan kula da lafiya da kuma daƙile yaɗuwar annobar Coronavirus tsakanin matafiya a filin jirgin.

Har ila yau Hukumomin filin jirgin sunce wannan sauka da jirgin ya yi a karon farko na a matsayin wata kwarya kwaryar buɗe filin jirgin, kafin a fara aiki gadan-gadan kamar yadda babban manaja a filin Gambo Abubakar Aboki ya shaidawa manema labarai.

Shima anasa ɓangaren mataimakin shugaba mai kula da yaɗuwar annobar Corona a jihar Kano Dr. Sabitu Shuaibu Shanono, ya bayyana irin matakan da gwamnatin Kano ta cika kafin amincewar gwamnatin tarayya a dawo da tashi da sauka na jiragen kasashen wajen a nan Kano.

Shanono ya ce “duk wanda zai tashi ya na da kyau ya je a gwadashi sannan suyi amfani da bada ta zara tare da saka ta kun kumin fuska wato face mask”

wasu daga cikin fasinjojin da suke shirin tafiya da kuma waɗanda suka sauka sun bayyana farin cikinsu game da dawowar tashin da saukar jiragen a jihar Kano.

A ya yin buɗe filin an tsaurara matakan kula da lafiya domin gudun yaɗuwar annobar corona da a baya ta haddasa garƙame filin sauka da tashin jiragen saman na Malam Aminu Kanon.

A baya dai Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar Litinin, 5 ga watan Afrilu, a matsayin ranar dawowa, amma daga bisani aka kara matsawa da ita zuwa 6 ga Afrilu 2021, sakamakon ranar ta zo a cikin ɗaya daga ranakun bukukuwan Ista.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan