Gwamna Ganduje zai gabatar da Ahmed Musa ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars

123

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta amince da yarjejeniyar sa hannu da kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa har zuwa ƙarshen kakar wasa na bana.

Idris Malikawa, jami’in yada labarai na kungiyar, a wata sanarwa da fitar a ranar Talata a Kano ya bayyana cewa shugaban kungiyar, Surajo Shuaibu ne ya sanar da cinikin.

A cewar Idris, bayan kammala cike dukkan ƙa’idoji, Gwamna Abdullahi Ganduje ne zai gabatar da ɗan wasan gabanin fara matakin rukuni na biyu na gasar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan