Ma’aikatan Shari’a Na Najeriya Za Su Yi Zanga-zangar Lumana

97

Ƙungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Najeriya, JUSUN, ta ce za ta yi zanga-zangar lumana a dukkan faɗin Najeriya ranar 19 ga Afrilu don tilasta wa gwamnati ta biya mata buƙatarta samun ‘yancin kuɗi.

Wannan barazanar zanga-zanga tana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Najeriya, NAN, ya samu a Lagos mai ɗauke da kwanan watan 16 ga Afrilu, wadda Mataimakin Sakataren Ƙungiyar, Mr P. Nnamani ya sanya wa hannu.

NAN ya rawaito cewa a ranar 6 ga Afrilu, JUSUN ta fara yajin aiki, inda ta yi kira da a samar mata da ‘yanci ta ɓangaren kuɗi.

JUSUN ta yi kira ga mambobinta da kar su canza ra’ayi duk irin matsin lambar da za su fuskanta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan