An ƙirƙiro Manhajar Bayar Da Bayanai A Kan Cutar Korona

116

Ƙungiyar Translators Without Boarders (TWB) ta ƙirƙiri wata manhaja da zata dinga taimakawa wajen bayar da bayanai tare da amsa tambayoyi game da cutar Korona, a cikin harshen Turanci da Hausa da kuma Kanuri.

Jami’i na musamman a ƙungiyar Ibrahim El-Yakub, ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai, inda ya ce manhajar da su ka ƙirƙira sun faɗa mata suna Shehu, da hakan ke nufin fasihin Mutum.

“Muna farin cikin gabatar da ‘Shehu’ a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Muna fatan bayanan da ke ciki za su taimakawa mutane wajen neman abin da su ke buƙata cikin harsunan su”

“Muna son jan hankalin masu ayyukan tallafawa jama’a a yankin arewa maso gabashin Najeriya, da su ƙirƙiro manhaja irin wannan don sauƙaƙa musu wajen ayyukansu da kuma al’ummar yankin,” In ji Ibrahim El-Yakub.

Manhajar Shehu da TWB su ka Ƙirkiro

Tun da farko an tattara bayanan da su ka shafi cutar Korona ta yadda mutane za su iya yin tambayoyi ga manhajar, sannan ta ba su amsa nan take. Alal misali mutum zai iya neman bayanai kan yadda zai kare kansa daga cutar da kuma matakan da suka da ce mutum ya bi idan ya kamu da cutar.

Haka kuma an sauƙaƙa bayanan da ke cikin manhajar, ta yadda suke da sauƙin fahimta ga wanda yake neman bayanai game da cutar ta Korona.

Ibrahim El- Yakubu ya ƙara da cewa “Manhajar Shehu ta shiga sahun jerin manhajoji da ƙungiyar ta ƙirƙira da ke ayyuka cikin harsuna daban-daban dominn bunƙasa ayyukansu a yankin”.

Ƙungiyar Translators Without Boarders (TWB) ƙungiya ce da ke tallafawa mutane a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yankin da ke fama da rikicin Boko Haram da ya ɗauki tsawon shekaru.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan