Home / Labarai / Umar Usman Kadafur ya zama muƙaddashin gwamnan Borno

Umar Usman Kadafur ya zama muƙaddashin gwamnan Borno

Majalisar Dokokin Jihar Borno ta amince da buƙatar Gwamna Babagana Umara Zulum inda ya nemi a naɗa mataimakinsa, Umar Usman Kadafur, a matsayin mauƙaddashinsa.

Zulum ya miƙa wannan buƙata ga majalisar ne domin ba shi zarafin tafiya hutu na kwana 21, kama daga ranar 29 ga Afrilu zuwa 19 ga Mayu, 2021.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Abdulkarim Lawan, ya ce tun a ranar 23 ga Afrilun da ya gabata gwamnan ya miƙa wa majalisar wasiƙar wannan buƙatar tasa, yana mai neman majalisar ta ba shi damar tafiya hutu na kwanaki 21.

Kazalika, Shugaban Majalisar ya ce gwamnan ya buƙaci majalisar ta amince ta naɗa Mataimakin Gwamnan jihar a matsayin Muƙaddashin Gwamna domin ba shi ƙarfin riƙon ragamar shugabancin jihar Borno, wanda hakan ya yi daidai da sashe na 190 (1) na Kundin Tsarin Mulki.

A ƙarshe Gwamna Zulum, ya umarci mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau, ya sanar da ‘yan jihar wannan batu. Tare da kira ga ɗaukacin jami’ai da ma’aikatun gwamnatin jihar, da su bada cikakken haɗin kai ga wannan sauyi da aka samu.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Shugaban riƙon ƙwaryar gwamnatin ƙasar Chadi ya ziyarci Mohamed Bazoum

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwaryar kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby lokacin da ya kai wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *