Home / Labarai / Wajibi ne Najeriya ta rungumi tsarin aikin ɗan sanda na al’umma – Atiku Abubakar

Wajibi ne Najeriya ta rungumi tsarin aikin ɗan sanda na al’umma – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamanatin Najeriya ta rungumi tsarin aikin ɗan sanda na al’umma domin magance ƙalubalen tsaro da ƙasar nan ke fama da shi.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a cikin sakon ta’aziyyar da ya miƙa ga iyayen yaron da wani tsohon jami’an soja ake zargin ya hallaka wani Yaro mai kimanin shekaru biyar (5), bayan ya karbi kuɗin fansa daga iyayensa, a shafinsa na facebook.

Na yi mutukar bakinci da jin labarin sace matashin nan Ahmad Kabir, wanda daga bisani aka tsinci gawar sa a cikin magudanar ruwa, bayan iyayen sa sun biya kudin fansa Naira miliyan biyar”

Ba zai yuwu mu ci gaba da rayuwa haka ba, Wajibi ne Najeriya ta rungumi tsarin aikin ‘dan sanda na al’umma, wanda zai dace da muradun “Yan kasa, domin magance matsalar rashin tsaro” In ji Atiku Abubakar

Batun kafa rundunar ƴan sanda mallakar jihohi a ƙasar nan a iya cewa yana daga cikin abin da ake tafka mahawarar akan sa a fagen siyasar kasar nan, inda wasu yan Najeriya na ganin cewa lokaci yayi da za a samu ƴan sanda ƙarƙashin ikon jihohi, don taimakawa rundunar ‘yan sandan dake karkashin ikon gwamnatin tarayya.

Masana harkokin tsaro dai da masu sharhi akan al’amuran yau da kullum na kallon gazawa ko raguwar tasirin da jami’an ‘yan sandan da ake da su a Najeriyar ne dai ya fara taso da buƙatar samar da ƴan sanda na jihohin, lamarin da ya kai ga matsin lamba biyo bayan yawaitar munanan kasha-kashen da ake fuskanta a sassan ƙasar nan.

Haka kuma matsalar rashin tsaro ta kai ga babu birni ba kauye, kisan jama’a da sace su ne kawai ake yi ba tare da hukunta masu laifi ba.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Shugaban riƙon ƙwaryar gwamnatin ƙasar Chadi ya ziyarci Mohamed Bazoum

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwaryar kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby lokacin da ya kai wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *