Home / Labarai / Yau ta ke ranar ƴan jarida ta duniya: Jaafar Jaafar ya yi gudun hijira zuwa ƙasar Burtaniya

Yau ta ke ranar ƴan jarida ta duniya: Jaafar Jaafar ya yi gudun hijira zuwa ƙasar Burtaniya

A daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 3 ga kowanne watan Mayu a matsayin ranar Ƴan Jaridu ta Duniya domin tunawa da karramma ‘Yan Jaridun da suka rasa rayukansu bisa gaskiya a bakin aiki, da kuma wadanda suka fuskanci cin zarafi ko tauye hakki, a wannan lokacin mawallafin jaridar Intanet ta Daily Najeriya wato Jaafar Jaafar ya yi gudun hijira daga Najeriya zuwa ƙetare sakamakon barazana da ya ke fuskanta.

Jaafar Jaafar shi da iyalansa na fuskantar barazanar da ta sanya shi arcewa daga Najeriya zuwa ƙasar Burtaniya domin samun nutsuwar da za ta ba shi damar gudanar da aikin sa cikin kwanciyar hankali ba tare da fuskantar wani ƙalubale.


A cikin wata hira da yayi da jaridar PREMIUM TIMES a jiya Lahadi, Jaafar ya bayyana cewa hankalin sa ba a kwance ya ke ba a kullum a kasar nan tun bayan ganowa da yayi lallai ana farautar sa.

Ba zan dawo Najeriya ba sai na samu tabbacin cewa gwamnati za ta samar mini da tsaro da iyalai na da kuma bani dama a matsayina na dan jarida in rika aiki na kamar yadda doka ta bani”

A cikin watan Afirilu ne ɗan jaridar ya sanar da cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya na neman sa ruwa a jallo saboda ya bidiyon da ya wallafa na karbar cin hanci daloli da aka nuna gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na karɓa.

Cin zarafi da kai hari kan ƴan jaridu don sun gudanar da aikinsu na zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke fuskantar aikin jarida a Najeriya, wanda ake ganin karuwarsa a sassa daban–daban na kasar nan inda daga faɗin gaskiya ko kuwa bankado wani zargi na aikata ba dai dai ba, ake kai musu hari, baya ga barazana ko kokarin rufe musu baki.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Shugaban riƙon ƙwaryar gwamnatin ƙasar Chadi ya ziyarci Mohamed Bazoum

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwaryar kasar Chadi Janar Mahamat Idriss Deby lokacin da ya kai wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *