Wasiƙa zuwa ga marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua

    200

    Bayan gaisuwa tare da fatan kana cikin dausayin rahamar ubangiji, Allah ya sa haka Amin.

    A yau 5 ga watan Mayun shekarar 2021 ka ke cika shekaru 11 da amsa kiran mahaliccinmu. Tabbas ƴan Najeriya mun yi rashin nagartaccen shugaba, adali, mutum mai gaskiya da ƙoƙarin kamanta ta, shugaba masanin harkokin mulki da yin abin da ya kamata, shugaba mai ilimi da hangen nesa.

    A yayin da nake rubuto maka wannan wasiƙa idanuwa cike suke da hawaye masu zafi, yayin da zuciya ta ke ƙuna da raɗaɗin irin halin da ƙasar da kake ƙauna da son ganin cigabanta, ƙasar da ka yi ƙoƙarin ɗorata a mizani na ƙwarai a lokacin rayuwar ka, sai dai kash yanzu kam ta ɗauko hanyar wargajewa, domin abubuwa sun taɓarɓare.

    Na rubuto maka wannan wasiƙar ne domin bayyana irin juyayi da halin zullumi, fargaba da zaman ɗar-ɗar da ƴan Najeriya musamman yankin Arewa su ka tsinci kansu bayan rasuwarka, wannan ya faru ne sakamakon facali da aka yi da kyawawan manufofin ka.

    Ko da ya ke nasan wasiƙata ba za ta riske ka ba, amma ina da yaƙinin za ta kai ga iyali da masoyanka masu kishi da son cigaban ƙasar nan, waɗanda suke maka addu’a a ko da yaushe, kuma shakka babu addu’o’in mu za su riske ka In Sha Allah, domin ka nuna mana ƙauna, ka kuma so cigaban mu shiyasa zuƙatan mu ke cigaba da begen ka har yanzu.

    Kamar yadda ƴan Najeriya za su yi maka shaida a ranar gobe ƙiyama akan yadda ka bijiro da ƙudurori guda bakwai (7), lokacin da ka hau kujerar shugabancin Najeriya, wato Seven Points Agenda, waɗanda ka bijiro da su da nufin kai ƙasar zuwa ga tudun mun tsira.

    Ƙudurorin su ne:

    • Haɓaka wutar lantarki
    • Wadatar da ƙasa da abinci
    • Haɓaka arzikin ƙasa
    • Inganta harkokin sufuri
    • Garanbawul kan yadda ake mallakar filaye
    • Samar da tsaro
    • Inganta Ilimi

    Sai dai kash, an yi watsi da waɗannan ƙudurori naka masu matuƙar alfanu bayan rasuwarka.

    A yau an wayi gari yankin arewacin Najeriya musamman mahaifarka da jihar ka ta zama wato Katsina da Kaduna sun zamo sansanin ƴan bindiga da ƴan fashin daji, rayuwa ta zama babu tabbas a waɗannan jihohi, manoma sun yi watsi da gonakinsu, ƴan kasuwa masu safara sun haƙura da yin safara saboda rashin tabbas akan lafiya da rayuwa, iyaye na fargabar tura ƴaƴansu zuwa makaranta.

    Kashe-kashe da zub da jini da tashe-tashen hankula sun zamo ruwan dare a yankin arewacin Najeriya lamarin da ya kai ga dawo da hannun agogo baya a dukkanin wata harka ta cigaba, satar ɗalibai a makarantu ta zama tamkar ruwan dare, a kullum babu abin da kafafen yaɗa labarai ke rawaitowa game da jihar ka ta haihuwa sai an kashe mutane adadi kaza…, an ƙone gari kaza, an yi garkuwa da ɗalibai kaza da sauran abubuwa marasa jin dadi.

    Marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua

    Allah ya sa kana Aljanna Firdausi Malam Umaru, yau an wayi gari yankin arewacin Najeriya musamman jihohin Katsina da Kaduna da kuma Zamfara na ƙoƙarin zama kufai saboda matsalar tsaro da ta addabi yankin. Iyaye sun rasa ƴaƴansu, Mata sun zama Zawarawa, Ƴaƴa sun zama marayu, ƙauyuka sun zama kufai sakamakon gudun hijira da al’umma ke yi saboda masifar rashin tsaro.

    Allah ya kyauta makwancinka Malam Umaru Musa Yar’adua, haƙiƙa ka zo da ƙoƙarin inganta tattalin arzikin Najeriya ta hanyar samar da isasshiyar wutar lantarki, wanda hakan zai farfaɗo da masana’antun ƙasar nan ƴan ƙasa su samu ayyukan yi, inganta harkar sufuri ta hanyar samar da ingantattun hanyoyi, amma kash yanzu abin ba haka ya ke ba. Domin a kullum harkar wutar lantarki a kasar nan ƙara ci baya ta ke yi domin kullum ƙara zama a cikin duhu ake yi, hanyoyin mu sun zama tarkon mutuwa, saboda rashin kyawu da inganci.

    Yau an wayi gari Najeriyar da kake fatan ganin ta shiga cikin manyan ƙasashe irinsu Brazil da India wajen ƙarfin tattalin arziki da cigaba, yau tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa da addini da kabilanci da kuma rashin ƙwarewar masu jan ragamar mulkin kasar tana kokarin zama sansanin yaƙi.

    A kullum rahotannin da ke fitowa daga yankuna daban-daban na ƙasar nan babu daɗin ji, an kashe mutane kaza, an ƙone caji ofis din yan sanda kaza, an kai hari gidan gwamnati kaza, an yi garkuwa da Ɗaliban Makaranta kaza, an kashe jami’an ƴan sanda ko Sojoji da sauran abubuwan da ke mayar da hannu agogo baya.

    Labarin wasiƙar tawa cike take da baƙin labarai masara daɗin ji ga mu da muke raye a nan duniya, amma dai babban labari mai daɗin ga reka shi ne, tabbas ƴan Najeriya za mu cigaba da yin jimamin rasuwarka Malam Umaru Musa Yar’adua musamman kasancewar ka gwamna da shugaban kasa na farko a Najeriya da ka fara bayyana kadarorinka, da hakan ke ƙara tabbatar da ƙyamar ka ga cin hanci da rashawa a tsakanin masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya.

    Da ana kiranye lallai da munyi maka, dama an ce ba rabo da gwani ba… Kuma ga shi muna tuna Bara, wanda hakan ke tabbatar da cewa ba mu ji daɗin bana ba.

    Amma zaka ji ni da wani sabon labarin nan gaba idan wasu abubuwa sun sauya.

    Ina fatan za ka cigaba da kasancewa cikin salama da dausayin rahamar ubangiji.

    Buhari Abba Rano, ɗan jarida ne kuma mataimakin mai bincike a Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma CITAD, Kano.

    Turawa Abokai

    RUBUTA AMSA

    Rubuta ra'ayinka
    Rubuta Sunanka a nan