Ɓarayin Waya A Kano Sun Kashe Wani Ma’aikaci Bayan Sun Sace Wayarsa

106

A ranar Asabar da yamma ne wasu ɓarayin waya a Kano suka kashe wani mutum mai suna Umar Muhammad, ma’aikacin Hukumar Kula da Kayan Tarihi ta Kaduna.

Wannan al’amari ya faru ne a gadar da ake kan ginawa a kasuwar Kantin Kwari dake cikin birnin Kano.

Wani shaidar gani da ido ya ce ya hango wani mutum yana ta fama tsakanin wasu ɓarayi da suke ƙoƙarin ƙwace masa waya.

Shaidar gani da idon ya ƙara da cewa a lokacin ne ne ɓarayin suka caka wa marigayi Umar wuƙa a wuya, abin da ya ja hankalin jama’a a lokacin da mamacin yake kwance cikin jini.

“Sai mutumin ya faɗi nan take ya suma, jini yana ta fitowa daga wuraren da ya ji rauni, ɓarayin kuma suka ranta a na kare da wayar da suka sace”, in hi shaidar gani da idon.

An gano cewa wasu mutanen kirki ne suka garzaya da marigayi Umar zuwa wani ofishin ‘yan sanda.

Daga nan ne su kuma ‘yan sandan suka garzaya da marigayin ɗan shekara 50 zuwa Asibitin Ƙwararru na Abdullahi, inda likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu.

‘Yan uwan marigayin sun ce a ranar Asabar ne marigayin ya ɓata, suka fara neman sa ranar Lahadi.

Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar al’amarin bayan ya tuntuɓi Ofishin ‘Yan Sanda na Ƙoƙarin Wambai.

DSP Abdullahi ya ce rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gano ɓarayin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan