Gwamnatin Buhari Na Yunƙurin Fitar Da Gajiyyayu Daga Ƙunci

125

Hukumar Kula da Mutane Masu Buƙata ta Musamman, NCPWD, ta fara tattara bayanan mutane masu buƙata ta musamman har su miliyan 31 don kyautata rayuwarsu.

Shugaban Hukumar, James Lalu ne ya bayyana haka a yayin wani taro don tattauna tasirin COVID-19 akan mutane masu buƙata ta musamman.

Ya ce za a tattara bayanan ne a dukkan jihohi 36 na Najeriya da kuma Birnin Tarayya, Abuja, FCT.

Ya ce za a fara tattara bayanan nan ne tun daga ƙauyuka har zuwa birane.

Mista Lalu ya ce burin hukumar shi ne ta tabbatar da an shigar da mutane masu buƙata ta musamman cikin gwamnati don su ma su bayar da gudummawarsu wajen ci gaban ƙasa.

Mista Lalu ya ce wannan yunƙuri na hukumar somin-taɓi ne kawai.

A cewarsa, wannan yunƙuri yana daga cikin alƙawuran da Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi na fitar da mutane miliyan 100 daga cikin talauci nan da shekara 10.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan